Ladan Wapa Ya Yaba Ayyukan Gwamna Dikko Radda, Ya Buƙaci Goyon Bayan Al’ummar Katsina



Alhaji Ladan Wapa Ya Yaba Salon Shugabancin Gwamna Dikko Radda, Ya Buƙaci Al’ummar Katsina Su Ba Shi Goyon Baya


Daga: Reality News TV, Katsina






Alhaji Ladan Wapa ya bayyana gamsuwarsa da salon shugabancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, inda ya roƙi al’ummar jihar da su bai wa gwamnatinsa cikakken goyon baya domin ƙara samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.


Alhaji Ladan Wapa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Reality News TV a Katsina. Ya ce irin shugabancin da Malam Dikko Radda ke yi ya nuna kishin ƙasa, gaskiya da kuma rikon amana, wanda a cewarsa hakan ne tushen cigaban kowace al’umma.


Ya ƙara da cewa, “Insha Allah, muna da cikakken tabbaci cewa idan Malam Dikko Radda ya samu damar komawa kan mulki a karo na biyu, zai sauya fasalin Katsina gaba ɗaya, har ta zama kamar wata London, ganin irin abubuwan da ya fara aiwatarwa a ƙasa.”


Alhaji Ladan Wapa ya jaddada cewa Gwamna Radda mutum ne mai hangen nesa, wanda ke aiki da gaskiya da tsoron Allah, yana kuma fifita muradun al’umma sama da komai.


Haka kuma, ya yabawa Gwamnan bisa yadda ya iya haɗa kan manyan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Katsina, lamarin da ya ce ya taimaka matuƙa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.


A ƙarshe, Alhaji Ladan Wapa ya yi fatan alheri ga Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya da hikima, sannan Ya albarkaci al’ummar Jihar Katsina .

Previous Post Next Post

نموذج الاتصال