Sabuwar Dokar Tsarin Fansho: Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar da Maidawa Wasu Ma’aikata Kuɗaɗen da Aka Cire Musu
Katsina — Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da shirin ta na maidawa ma’aikatan da suka kusa yin ritaya kuɗaɗen da aka riga aka cire daga albashinsu domin ajiyar fansho, sakamakon sauyin fasalin sabuwar dokar tsarin fansho da jihar ta amince da ita.
Sabuwar Hukumar da Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin aiwatar da dokar fanshon da aka yi wa garambawul ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin inganta rayuwar ma’aikata bayan ritaya tare da kawar da matsalolin jinkiri da rashin tabbas wajen biyan haƙƙoƙinsu.
Babban Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Fansho ta Jihar Katsina, Alhaji Nuraddeeni Audi, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Katsina.
Tsari Uku a Sabuwar Dokar Fansho
Alhaji Nuraddeeni Audi ya bayyana cewa sabuwar dokar fansho, wadda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanya wa hannu kuma ta fara aiki a watan Nuwamba da ya gabata, ta kasu kashi uku:
- Ma’aikatan da shekarun aikin da suka rage musu ba su kai shekara biyar ba;
- Ma’aikatan da ke da tsakanin shekara biyar zuwa talatin na sauran shekarun aiki;
- Ma’aikatan da ke da sama da shekara talatin na sauran shekarun aiki, ciki har da sabbin ma’aikata da za a ɗauka nan gaba.
Dalilin Maidawa Wasu Kuɗaɗe
Babban Daraktan ya ce za a maidawa ma’aikatan da shekarun aikin da suka rage musu ba su kai shekara biyar ba kuɗaɗen da aka cire daga albashinsu, tare da dakatar da ci gaba da cire musu kuɗin, kasancewar sabuwar dokar ta fitar da su daga tsarin fanshon da aka gyara.
Ya ce an ware wa irin waɗannan ma’aikata, da kuma tsofaffin da ke karɓar fansho, wata hukuma ta daban da za ta ci gaba da kula da haƙƙoƙinsu tare da biyan fansho kamar yadda tsarin jihar yake a halin yanzu.
Alhaji Nuraddeeni Audi ya ƙara da cewa akwai yiwuwar ma’aikatan su samu ƙarin kuɗi sama da abin da aka cire musu, bisa ribar da aka samu daga ajiyar kuɗaɗen.
Tsarin Taimakon Juna ga Ma’aikata
Game da ma’aikatan da ke da tsakanin shekara biyar zuwa talatin, Babban Daraktan ya tabbatar da cewa fansho da gratuti ɗinsu ba zai yi ƙasa da abin da ake samu a yanzu ba.
Ya bayyana cewa ma’aikata za su rika bayar da wani kaso daga albashinsu, yayin da gwamnati ma za ta rika bayar da nata kaso, ana haɗa su domin tabbatar da cewa ma’aikaci zai karɓi gratuti da fansho nan take bayan ritaya, ba tare da jinkiri ba.
A cewarsa, tun farkon shekarar nan aka fara cire kashi 7 cikin 100 daga albashin ma’aikata, yayin da gwamnati ke bayar da kashi 13 cikin 100, wanda ya kai kashi 20 cikin 100 gaba ɗaya.
Tsarin Zamani Irin na Tarayya
Dangane da kashi na uku, wato ma’aikatan da ke da sama da shekara talatin zuwa ritaya, Alhaji Nuraddeeni Audi ya ce tsarin su ma na taimakon juna ne tsakanin ma’aikaci da gwamnati.
Ya ce an gina tsarin bisa salon zamani irin na gwamnatin tarayya, inda ƙwararrun kamfanonin kula da fansho da gwamnati ta tantance za su rika kula da ajiyar kuɗaɗen, domin kare makomar ma’aikata bayan ritaya.
Martani kan Jita-jita
Babban Daraktan ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa sabuwar dokar za ta janyo karɓar fansho ƙasa da kima, yana mai cewa tuni dokar ta magance duk wata barazana ga haƙƙin ma’aikata.
Ya buƙaci ma’aikatan jihar da su guji yaɗa jita-jita marasa tushe, yana mai jaddada cewa an tsara dokar ne domin kwantar da hankalin ma’aikata da tabbatar da walwalarsu bayan ritaya.
Godiya ga Gwamna
A ƙarshe, Alhaji Nuraddeeni Audi ya gode wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, bisa aiwatar da sabuwar dokar cikin natsuwa da gaskiya.
Ya ce matakin wata babbar shaida ce ta ƙoƙarin gwamnatin jihar na gina kyakkyawar makoma ga ma’aikatan Katsina.
